Kotu Ta Ba da Belin Mawallafin Jaridar Wikki Times Da Gwamnan Bauchi Yasa A Kama
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare ta bayar da belin Haruna Mohammed mawallafin wata jarida ta yanar gizo ta Wikki Times da ke Bauchi, har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan tuhumar da ake yi masa na tada zaune tsaye, da hargitsin zaman lafiyar al’umma da kuma bata wa Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed suna.
A ranar Laraba ne dai aka bayar da belinsa amma ya kasa cika sharuddan inda ake bukatar hakimi da ke karkashin ikon kotu da kuma babban ma’aikacin gwamnati zuwa mukamin darakta a matsayin wanda zasu tsaya masa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin da yasa Obi ya fice daga PDP ya koma Labour Party – Atiku
A lokacin da wanda ake tuhumar ya kasa cika sharuddan, a ranar Alhamis ne kotun ta bayar da sauye-sauye na sharuddan belin tare da maye gurbin hakimin da shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Bauchi wanda hakan ya sa aka sake shi.
An tasa keyar mawallafin a gidan yari a ranar Talata bayan da ‘yan sanda suka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da daukar wasu mata hayar da za su tayar da hankali ta hanyar tunzura mutane da yin kalaman da za su kawo illa ga zaman lafiya da walwalar wadanda suka yi yi niyyar kada kuri’a a mazabar Duguri a karamar hukumar Alkaleri.
An kuma gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin yi wa gwamnan ɓatqnci a unguwar sa, sabanin sashe na 114 na kundin laifuffuka.
Lokacin da aka ambaci karar a ranar Talata, wanda ake zargin (Mohammed) ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Babban lauyan gwamnatin jihar ya nemi karbar karar daga hannun ‘yan sanda kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 ya kunsa.
Alkalin kotun, Ahmed Musa, ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Maris.
A wani labarin kuma: Sakamakon zabe: Dole daya daga cikin Maƙaryaci ne — Oshiomhole ga Atiku, Obi
Tsohon Gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ko dai Atiku Abubakar ko Peter Obi na karyar ikirarin nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
‘Yan takarar jam’iyyar PDP da na jam’iyyar Labour ta LP sun yi jawabi daban-daban a karon farko a ranar Alhamis bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana sakamakon zaben a ranar Laraba.