Wata babbar kotu da ke zamanta a Minna a jihar Neja, ta bayar da sammacin kamo babban hafsan sojin kasa, Janar Faruk Yahaya bisa zarginsa da laifin sabawa Umarnin kotu, bisa umarnin Mai shari’a Halima Abdulmalik. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Haka kuma lamarin ya shafi Kwamandan Horar da Rukunan soji dake Minna, Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ronaldo Na Daf Da Cimma Yarjejeniya Da Wata Kungiya A Kasar Saudiyya
Babban alkalin jihar, Halima Abdulmalik, ta bayyana cewa, umarnin ya biyo bayan sauraron karar da aka shigar gaban kotun, bisa ga doka ta 42, doka ta 10 na dokar kare farar hula ta babbar kotun jihar Neja ta shekarar 2018.
Mai shari’a Halima Abdulmalik ta bayyana cewa: “Kotu na bukatar shugaban hafsan sojin kasa, Janar Faruk Yahaya da kwamandan horas da sojojin na Minna, Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji, a tsare a gidan yari na Minna domin sabawa umarnin wata kotu a ranar 12 ga wata. Oktoba 2022.
Ta ba da umarnin a ci gaba da tsare mutanen biyu a gidan yari har sai sun wanke kansu daga zargin sabawa umarnin kotu.
Sai dai daga Bisani, Alkalin da ke jagorantar shari’ar ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Disamba 2022 don ci gaba da sauraron karar.
A wani labarin kuma, Rundunar Ƴan Sanda ta ƙaryata rahoton bazuwar ƴan ta’adda a Abuja
Rundunar Ƴan sandan babban birnin tarayya ta karyata rahotannin da ake yadawa cewa masu aikata laifuka na Bazama a babban birnin kasar.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa rahoton na daga cikin miyagun abubuwa, inda ya jaddada cewa ba shi da gaskiya