Mai shari’a Olubunmi Abike-Fadipe ta wata kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja a ranar Juma’a ta umurci sufeto-janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba da ya kamo wasu ‘yan kasuwa uku da ake zargi da wawure katan 245 na kayan kwalliya na Naira miliyan 19.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Fadipe ta bayar da umarnin a gurfanar da wadanda ake zargin, Tunde Yusuf, Adebayo Dayo da kuma Michael Obisiji a gaban kotu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Duminsa: Gwamna Wike Ya Kara Yawan Sabbin Mataimakan da Ya Naɗa Zuwa 200,000
Ta bayar da umarnin a kamo mutanen uku, biyo bayan rashin zuwan su domin gabatar da karar da I-G ta shigar a gabansu ta hannun rundunar CID da ke Alagbon a Legas.
Ta umurci ‘yan sanda da su kamo wadanda ake tuhuma kafin ranar da za a ci gaba da zaman kotun.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Lauyan mai gabatar da kara, ACP Morufu Animashaun, ya shigar da kara mai lamba LD/13338C/2020, inda ya yi zargin cewa wadanda ake zargin da sauran su a wani lokaci a cikin watan Maris shekarar 2020 a tashar jirgin ruwa ta Apapa Tin-Can, sun sace kwali 245 na kayan kwalliya, kadarorin Remiginus Okafor.
Animashaun ya sanar da kotun cewa bai san inda wadanda ake zargin suke ba lokacin da aka kai karar.
“Ba mu iya samun su ba ya mai shari’a.
“An mayar da tawagar binciken daga hurumi saboda rashin tsaro a kasar,” in ji shi.
Mai gabatar da kara ya shigar da tuhume-tuhume guda biyu da suka hada da hada baki wajen aikata manyan laifuka: sata a kan wadanda ake tuhumar.
A cewar sa, laifin da ake zargin su dashi ya sabawa tanadin sashe na 287(5) da 411 na dokokin laifuka na jihar Legas shekarar 2015.NAN.
A wani labarin kuma, UNICEF Ta Bukaci A Ceto Yara 21 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a ranar Juma’a ya bukaci hukumomi da su tashi tsaye wajen ceto yara 21 da aka sace a wata gona a unguwar Mairuwa da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa da wakiliyar UNICEF a Najeriya, Misis Cristian Munduate ta sanya wa hannu, hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana sace yaran a matsayin wani “abin zargi”.