Wata babbar kotun jihar Kaduna a ranar Talata ta dage shari’ar da tsohon dan majalisar sarkin masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu ya shigar, ta neman a tsige Sarkin Zazzau na 19, Ahmed Nuhu Bamalli daga matsayin sa,kamar yadda Punch ta rahoto.
Tsohon dan majalisar sarkin wanda ya halarci nadin sarkin ya kai gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da wasu mutane 13 gaban babbar kotun jihar inda yake neman a tsige Bamalli daga matsayin Sarkin Zazzau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Kalu Ya Janye Daga Neman Kakakin Majalissar Najeriya
Daga cikin mutane 13 da ake kara a shari’ar sun hada da Sarki Ahmed Nuhu Bamalli, da marigayi Limamin Kona, Malam Sani Aliyu, wanda ya rasu a watan Yulin shekarar 2021.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa gwamna Nasir El-Rufai ya nada Ahmed Nuhu Bamalli, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Thailand a matsayin Sarkin Zazzau na 19 a ranar Laraba 7 ga watan Oktobar shekarar 2020 bisa shawarar da masu zabar sarkin masarautar Zazzau suka ba shi.
Aminu wanda ya rike mukamin Wazirin Zazzau, mukamin da ya ba shi damar zama daya daga cikin masu masu zabar sarki, yana neman a soke nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli tare da tsige shi daga matsayin Sarkin Zazzau.
Lauyoyin wadanda ake kara sun shigar da kara na farko a gaban babbar kotu ta 4 karkashin jagorancin mai shari’a Isah Aliyu, inda suka ce kotun ba ta da hurumin sauraren karar, duk da cewa mai karar ba shi da wurin da zai kalubalanci nadin Sarkin.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kotun, lauyan masarautar Zazzau da kuma mai martaba Sarkin Zazzau, Abdul Ibrahim, SAN, ya ce suna kalubalantar matakin da mai shigar da karar ya dauka na kafa shari’ar saboda “ba ya cikin wani hukuncin da gidan masarautar Zazzau ta yanke kuma baya cikin masu neman takara a Masarautar.”
Ya ce, “Don haka, shi ba mamban gidan masarauta ba ne. Bai tsaya takara ba kuma yana mulkin mai kula da al’adar Masarautar Zazzau. Tuni aka cire shi a matsayin Hakimi a Masarautar.
“Har ila yau, kotu ba ta da hurumin sauraron wannan shari’a kuma mun shigar da kararrakinmu na farko kuma muna jiran hukuncin kotu kan hakan.
“Alkalin ya dage sauraren karar, amma bai bayar da ranar da za a yanke hukuncin ba tukuna.”
A nasa bangaren, lauyan mai kara, B.M Bello, ya ce wanda yake karewa yana kalubalantar cancantar Sarki Bamali, don haka yana son a soke nadinsa tare da tsige shi daga mukamin Sarkin Zazzau.
“Gaskiya muna kotu ne saboda muna kalubalantar nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau.
“Domin mun yi imanin cewa, kamar yadda aka ce, ba a bi dokokin da suka dace da al’ada wajen nadin nasa da hukuma ta yi ba,” inji shi.
A cewarsa, lauyoyin wadanda ake kara sun shigar da kara na share fage, ganin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar.
Bello ya kara da cewa, “Yanzu, kotu ta dage zamanta domin yanke hukunci kan lamarin, ko tana da hurumi ko a’a.”
A wani labarin kuma, Kasashen Kudancin Afrika Za Su Tura Dakaru Zuwa DR Congo
A ranar Litinin ce kasashen kudancin Afirka suka amince da tura dakaru don taimakawa wajen dakile tashe tashen hankula a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda kungiyoyi masu dauke da makamai suka addabi fararen hula tsawon shekaru da dama. Kamar yadda African News ta ruwaito.
Wani taron koli na kungiyar raya kasashen kudancin Afirka da ta gudanar karo na 16, wanda ya hada da Afirka ta Kudu, Angola, Mozambik da Tanzaniya, ya goyi bayan aikewa da dakaru “don maido da zaman lafiya da tsaro a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, in ji wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Windhoek babban birnin kasar Namibia.