Wata babbar kotun jihar Bauchi ta yankewa wani babban malami, Jalaludeen Zakari, hukuncin daurin shekaru 11 a gidan yari, bisa samunsa da laifin yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara shida da ke makarantar a wurin tantance masu neman shiga makarantar.
An ce wanda aka yanke wa hukuncin ya tsare yarinyar na tsawon sa’o’i da dama bayan kammala makaranta kafin ya aikata abinda ya aikata da ita.
Karanta nanYan Bindiga Sun Bukaci Naira Miliyan 50 Kafin Sakin Shugaban Karamar Hukumar Akwanga
Barista Dayabu Ayuba, lauya mai shigar da kara a ma’aikatar shari’a ta jihar ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar DAILY POST a Bauchi ranar Talata.
Ayuba ya ce a lokacin da ake shari’ar, shaidu uku, ciki har da wadda abin ya faru akanta sun bayar da shaida, wanda hakan ya sa aka yanke hukuncin.
Hakan yasa Alkalin kotun ya yankewa wanda aake zargi wannan hukuncin bayan Jalaludeen ya roki kotu da ta yi masa sassauci.
Mai laifin ya bukaci wadda aka azabtar da ta yafe masa,an tabbatar da cewar a lokacin da yake tantance daliban da zasu shiga makarantar.
Sai malamim ya umarci sauran daliban da su wuce ita kuma ta tsaya ba tare da bayar da dalilin tsawaita zamanta ba,yayin da aka bar ta a baya,wanda aka yane wa hukuncin ya yi mata fyade wanda kuma hakan babban laifine inji shi.
A wani labarin kumaGwamnatin Nijeriya Ta Dakatar Da Tantance Shaidar Digiri Daga Kasashen Benin Da Togo
Gwamnatin tarayya ta dakatar da tantancewa da kuma tantance takardun shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Talata ta hannun Misis Augustina Obilor-Duru, mataimakiyar daraktar yada labarai, ma’aikatar ilimi.
Wannan dakatarwar ta zo ne a sakamakon wani aikin bincike da wani dan jarida ya yi wanda ya kai ga buga jaridar Daily Nigerian a ranar 30 ga watan Disamba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wani dan jarida mai suna Mista Umar Audu ya gudanar da wani bincike mai suna “UNDERCOVER: Yadda wakilin jaridar DAILY NIGERIAN ya ba Cotonou varsity digiri a cikin makonni shida, ya shiga shirin NYSC