A ranar Juma’a ne wata kotun yanki da ke garin Jos ta yanke wa wani matashi mai suna Bulus Sunday dan shekara 20 da haihuwa, hukuncin zaman gidan yari na shekara daya ba tare da zabin tara ba bayan satar kayan firiji.
Alkalin kotun, Mista Shawomi Bokkos, ya yanke hukuncin ne ranar Lahadi bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Karanta nanSakin Nmadi Kanu Zai Magance Wasu Matsalolin Nijeriya–Meekam
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Insp Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 7 ga watan Satumba a ofishin ‘yan sanda na “A” ta hannun wani Pandong Demi, wanda ya shigar da kara.
Mai gabatar da kara ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa kai cikin gidan inda ya sace wasu firij da na’urorin sanyaya da kuma wayoyin wuta kafin jami’an tsaro su kama shi.
Gokwat ya ce laifin ya saba wa tanadin kundin hukunta manyan laifuka na jihar Filato. (NAN).
A wani labarin kuma
Barayi Suna Tursasa Mana Biyan Haraji Kafin Dibar Amfanin Gonarmu-Manoman Kaduna
‘Yan bindiga da ke addabar al’ummar Kaduna na tilastawa mazauna kauyukan biyan haraji kafin a bar su su girbe amfanin gona a gonakinsu a jihar.
An tilasta wa manoman da abin ya shafa daga kauyukan Kidandan da Galadima, yayin da kuma wadanda suka fito daga kauyukan Angular Fala’u da Kerawa ke ci gaba da muzgunawa tare da yin garkuwa da su yayin da suke aikin gonakinsu.
Wata majiya daga kauyen Kidandan ta bayyana cewa mutanensu, wadanda galibinsu manoma ne, suna biyan Naira 70,000 zuwa Naira 100,000 kafin su girbe amfanin gonakinsu.
Ya bayyana cewa wadanda suka ki biyan kudin, ko dai ana garkuwa da su, ko a kashe su ko kuma ‘yan fashin sun kwace amfanin gonakinsu.