By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun majistare dake zamanta a Ado Ekiti ta bayar da umarnin a tsare wani mai suna Olajiga Sikemi mai shekaru 31 tare da Olajiga Banji mai shekaru 63 da kuma Olajiga Victoria mai shekaru 57 a gidan yarin hukumar dake kula da aikin gyaran fuska ta Najeriya a Ado Ekiti.
Alkalin kotun, Michael Faola, ya bayar da umarnin da a ci gaba da tsare wadanda ake kara har sai an ba da shawarar lauyoyi daga ofishin daraktan kararrakin jama’a.
Dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Bamikole Olasunkanmi, yace wadanda ake tuhumar a ranar 6 ga watan Disamba, 2021, ana kyautata zaton sun aikata laifin kisa da sakaci, wanda ya kai ga mutuwar Demilade Fadare mai shekaru 7 a Unguwar Adehun ta dake Ado Ekiti.
A cikin sanarwar da ‘yan sandan suka fitar, mahaifin marigayin, Fadare Oluwasola, yace bayan neman Demilade daya je siyan pap din abincin karin kumallo a ranar data gabata, ya samu labari a ofishin ‘yan sanda cewa an tsinci gawar ‘yarsa a gidan makwabcinsu. cooler da alamun jininta a kasa.
Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraren karar har zuwa ranar 10 ga watan Janairun na sabuwar shekarar 2022 domin sake neman su.