Mai shari’a Adenike Akinpelu na babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin a ranar Talata, ya samu wani matashi Francis Stephen Oke Eghele mai shekaru 24 da haihuwa da laifin gabatar da kansa a matsayin mace Ba’amurkiya domin ya damfari wadanda ba a san ko su wanene ba.
An yanke masa hukuncin ne tare da wani Adeniyi Adekunle Aliyu daga Iworoko, Ado Ekiti, Irepodun/Ifelodun dake karamar hukumar Ifelodun ta jihar Ekiti bisa irin wannan laifin.
KARANTA WANNAN: Kogi: Kotu Ta Bayyana Wanda Zai Yiwa Jam’iyyar NNPP Takarar Gwamna
Rundunar hukumar EFCC ta shiyyar Ilorin ce ta gurfanar da Francis da Adeniyi a gaban kuliya, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.
Tuhumar laifukan 2 da ake wa Francis ya karanta:
“Cewa, kai Stephen Oke Eghele (wanda aka fi sani da Sugarmom) a wani lokaci a cikin watan Yulin shekarar 2022 ko kuma a garin Ilorin, jihar Kwara da ke karkashin ikon wannan kotun mai girma ka yi yunkurin aikata laifin zamba ta hanyar yin kama da wakiltar kanka a matsayin mace ba’amurkiya da ake kira da sugarmom wacce kuke soyayya da wani bature, Oliver Pedrin.
Tuhumar tace “Kamar yadda yake kunshe a cikin asusunku na Instagram: Sugarmomheater-0034 kuma ka aikata laifin da ya sabawa sashe na 95 na dokokin Penal Code na arewacin Najeriya.
A daya bangaren kuma, cikakkun bayanan tuhumar da ake yi wa Adeniyi sun hada da:
“Kai Adeniyi Adekunle Aliyu a wani lokaci a cikin watan Nuwambar shekarar 2022, a Ilorin, Jihar Kwara, da ke karkashin ikon wannan Kotun Mai Girma, ka yi damfara ta hanyar bayyana kanka a matsayin wata mata ba’amurkiyar mace mai suna Jessica Joanne da adireshin imel, wanda ka yi amfani da shi wajen sadarwa tare da wani Joe Maccreeary kuma ka sa shi ya aiko muku da jimilar kudi dala $200 ta Google play Giftcards kuma ta haka ne ya aikata laifin da ya saba wa sashe na 321 na Dokar Penal Code da Hukunci a karkashin sashe na 324 na wannan Dokar.
Mutanen biyu sun amsa laifinsu.
Biyo bayan karar da suka shigar Anselm Ozioko (Jnr) da Isabel Adeniran wadanda suka wakilci hukumar EFCC wajen gurfanar da su gaban kuliya sun bukaci kotunan da su hukunta wadanda ake kara bisa la’akari da karar da suka shigar da kuma shaidun da aka gabatar a gabanta.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Akinpelu ta yankewa Francis hukuncin daurin watanni shida kan kowance shari’a 1 da ta 2 tare da zabin biyan tarar N100,000 akan kowanne tuhume-tuhume.
Kotun ta kuma bayar da umarnin a baiwa gwamnatin tarayya wayar Infinix guda daya, wacce mai laifin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin.
Hakazalika, an yankewa Adeniyi hukuncin zaman gidan yari na watanni shida tare da zabin biyan tarar Naira N200,000.
Sannan kotun ta bayar da umarnin cewa, wayar Nokia guda daya, da kwamfutar tafi-da-gidanka hp, wayar Infinix da ya yi amfani da ita wajen aikata laifin da kuma kudi Naira 200,000 da ya ci gajiyar haramtattun ayyukan a ba wa gwamnatin tarayya.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Sakataren Jam’iyyar PDP Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam’iyyar
Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kwara, Alhaji Rasaq Lawal, ya yi murabus daga ofishin sa.
Alhaji Lawal ya sanar da yin murabus din sa ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon. Babatunde Mohammed a ranar Talata.