Wata babbar kotun jihar Kano ta hana gwamnatin jihar daukar duk wani mataki a kan makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu a jihar.
Mai shari’a Nasiru Saminu ne ya bayar da umarnin na hana gwamnati ci gaba da yunkurin daukar wani mataki a halin yanzu bayan sauraron karar da Barr AbdulHafees D. Khalid ya shigar yana neman kotun ta dakatar da gwamnatin.
Karanta nanKotu Ta Bayar da Umarnin Cafko Wani Dan Kasuwa Kan Zargin Almundahanar N4.8bn
Wadanda suka nemi a shigar da kara sun hada da kungiyar amintattu na kungiyar Model Islamic Schools, Nigeria, Incorporated Trustees of Independent School Proprietors’ Association Kano, Incorporated Trustees of the National Proprie of Private Schools Kano Chapter, Incorporated Trustees of Association of Private Schools.
Da kuma sauran mamallakan makarantu masu zaman kansu a fadin Jahar,inda suke bukatar gwamnatin ta dakatar da yunkurin hanasu lasisin gudanarwa kamar yada tayi niyyar yi.
Yayin da wadanda ake kara sun hada da gwamnatin jihar Kano, gwamnan jihar Kano, da babban lauyan gwamnatin jihar Kano, da hukumar kula da masu zaman kansu da ayyukan sa kai ta jihar Kano, da kuma Comrade Baba Abubakar Umar.
A wani labarin kumaGwamna Idris Ya Bukaci Hukumar FRSC Ta Kara Kaimi Wajen Rage Yawan Hadurra A Jahar Kebbi
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar da masu makarantu masu zaman kansu a jihar sun shiga fafatawa a kan batutuwan da suka dame su kan batun sabunta lasisin aiki da karin kudin makaranta da dai sauransu.
Inda gwamnatin ta dauki aniyar karbe lasisin duk wata makaranta mai zaman kanta a fadin Jahar har sai sun cika wadansu sharudda da ta gindaya masu.