Babbar kotun jihar ta hana jam’iyyar APC amincewa da Ishaku Abbo a matsayin dan takararta na Adamawa ta Arewa a zabe mai zuwa.
Mai shari’a Danladi Mohammed ya ce Sanata Abbo ba shi da hurumin sake neman tazarce tunda jam’iyyar ta kore shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban NNPP Ya Koka Kan Cin Kashin da Ake Wa Allunan Tallata Yan Takararsu a Borno
Alkalin wanda ya kuma hana Sanata Abbo bayyana kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar na shiyyar, ya kuma bayyana cewa, rikicin da ke tsakanin Sanata da APC na da nasaba da kudurin shugabannin kananan hukumomin Mubi ta Arewa na jam’iyyar mai dauke da kwanan wata 7 ga watan Oktoba 2022, wanda ya yi nuni da cewa, a cikin wannan rikici na jam’iyyar. ta kore shi kuma ta hana shi cin moriyar duk wani hakki ko wani gata da aka ba ‘yan APC.
Sai dai Sanata Abbo ya bayyana ci gaban a matsayin yanke hukunci a kan kudi. Ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa hukuncin ‘sayen sa akayi’ domin wadanda suka ce sun kore shi daga jam’iyyar ba shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi ba ne don haka ba su da hurumin yin hakan.
A cewarsa, shuwagabannin jam’iyyar a gundumomi ne kawai a tsarin mulkin jam’iyyar APC suke da hurumin hukunta duk wanda ya yi kuskure ba karamar hukuma ko ma ta jiha ba.
Abbo wanda ya bayyana cewa zai shigar da kara a kan hukuncin, ya kuma bayyana cewa, alkalin kotun ya taba bayar da umarnin haramtawa karamar hukumar bayyana kansu a matsayin exco.
A wani labarin kuma, Zaben Sanatan Borno Ta Tsakiya: Kotu Ta Tabbatar Da Kumaila A Matsayin Dan Takarar PDP
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta tabbatar da Mista Muhammed Kumaila a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben Sanatan Borno ta tsakiya.
Kotun, a hukuncin da mai shari’a Emeka Nwite ya yanke, ta yi watsi da karar da ta kalubalanci gabatar da sunan Kumaila ga hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da jam’iyyar ta yi.