By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Litinin din da ta gabata ce babbar kotun Benin ta kotun masana’antu ta Najeriya ta soke korar ma’aikatan kwalejin aikin gona taa jihar Edo da ke Iguoriakhi, tare da ba da umarnin biyan diyya naira miliyan 4m ga kowane ma’aikacin da abin ya shafa da kuma naira 500,000 ga kowanen su ta bata suna.
Ya yin yanke hukunci a cikin ƙarar mai lamba NICN/BEN/25/2018 tsakanin Mista Imhenrion Martin, Mista Adorolo Michael, Mista Osayande Clifford, Mrs Mercy Ozabor da Mista Eikhor Nosakhare Abel da kuma gwamnatin jihar Edo, kwamishinan noma da albarkatun kasa, babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a.shugaban Kwalejin aikin gona ta Iguoriakhi, da kuma majalisar gudanarwa na kwalejin, Justice Abiola Adewemimo ya ce a biya diyya ga ma’aikatan 90 da abin ya shafa cikin kwanaki 30 kuma idan ba a yi haka ba, adadin zai jawo riba a duk shekara na kashi 10 kan kowannensu.
Ta ce gwamnatin jihar ba daidai bane ta yi ikirarin cewa ma’aikatan na wucin gadi ne, saboda wasikun aikinsu na nuni da wani lokaci na jarabawa, wanda ta ce ba wai ma’aikata ne na wucin gadi ba.
Alkalin ya ce “Wannan kotun za ta duba rashin adalcin ayyukan kwadago kuma wadanda ake kara su ce aikin nasu na wucin gadi ne na rashin adalcin ayyukan kwadago,” in ji alkalin.
Ta ce duk da cewa ma’aikaci yana da hakkin ya daina aiki, dole ne a yi irin wannan aiki bisa ka’idojin da aka gindaya, babu abin da gwamnatin jihar bata yi ba a cikin lamarin.
Mai shari’a Adewemimo ya ce gwamnati ba ta nuna wata shaida da ke nuna cewa makarantar ba a yanzu take ba, amma ana yi mata gyaran fuska kuma zai yi wahala a maido da ma’aikatan kamar yadda aka bukata.
Ta ce ba za a iya biyan diyya na musamman ta fuskar albashi da karin girma da ma’aikata ke nema ba saboda ba su tabbatar da su da takardun da doka ta tanada don cin gajiyar irin wannan tallafin ba.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, lauyan ma’aikatan, Matthew Edaghese, ya ce a cikin hikimar kotun ta ce kawo karshen nadin ba komai bane, domin ta yi watsi da duk wasu sanannun dokokin aiki da suka dace.
“Wani rashin hankali ne na zartarwa. Wannan gargadi ne ga mambobin bangaren zartarwa na gwamnati cewa dokokin sun kasa ne suna tafiyar da su, kuma ba dokoki ne na kansu ba,” inji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ma’aikatan sun shigar da karar ne a watan Agustan shekarar 2018, sakamakon dakatar da nade-naden da gwamnatin jihar ta yi, inda ta ce tana sake fasalin hukumar.