- Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta soke takarar zababben gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti.
- Mai shari’a M N Yunusa ya kuma soke takarar duk wasu masu rike da tutar jam’iyyar Labour a jihohin Abia da Kano
- Alkalin ya yanke hukuncin ne bisa Gazawar jam’iyyar Labour wajen mika rajistar zama mambobinta ga hukumar zabe ta INEC cikin kwanaki 30.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta soke takarar zababben gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti,Punch ta rawaito.
Baya ga Otti, kotun da Mai shari’a M N Yunusa ke jagoranta ta kuma soke takarar duk wasu masu rike da tutar jam’iyyar Labour a jihohin Abia da Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Saudiyya Ta Raba Wasu Jariran Najeriya Biyu Da Aka Haifa Manne Da Juna
Yunusa ya yanke hukuncin cewa fitowar su bai dace da tanadin dokar zabe ta 2022 ba.
Alkalin ya yanke hukuncin ne a kan wata kara mai lamba FHC/KN/CS/107/2023 da wani Mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar a kan jam’iyyar Labour da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
“Jam’iyyar da ba ta bi tanade-tanaden dokar zabe ba, ba za a ce tana da dan takara a zaben ba, kuma ba za a iya bayyana cewa ta lashe zabe ba; saboda haka, kuri’un da aka baiwa wanda ake kara na 1, kuri’a ce da babu ita,” alkalin ya ce.
A cewarsa, gazawar jam’iyyar Labour ta mika rajistar zama mambobinta ga hukumar zabe ta INEC cikin kwanaki 30 kafin zaben fidda gwanin nasu ya sa tsarin ya zama mara inganci.
A wani labarin kuma, Har Yanzu Kotu Bata Bayyana Wanene Shugaban Najeriya Ba – Peter Obi Ga Amurka
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a babban zaben da aka kammala kwanan nan, Peter Obi, ya caccaki kiran da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony J. Blinken ya yi wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
A cewarsa, bai kamata kasar Amurka ta fara taya Tinubu murna ba, sakamakon yanzu haka batun zaben sa na gaban kotu.