Mai shari’a Bala Usman na babbar kotun tarayya da ke Jalingo ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta da kada ta tsayar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Taraba karkashin jam’iyyar APC a zaben da za a yi ranar 18 ga watan Maris.
Kotun ta sake tabbatar da Bwacha a matsayin zababben dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 18 ga watan Maris.
KARANTA WANNAN LABARIN: IWD 2023: Ku Kare Kuri’unku Don Ceto Dimokuradiyya — Wamakko Ga Matan Najeriya
Mai shari’a Usman ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a tabbatar da hukuncin kotun koli wanda ke da hukuncin da ya sa jam’iyyar APC ta sake yin sabon zaben fidda gwani inda Emmanuel ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Kotun ta tabbatar da takarar Bwacha ne yayin da ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar na neman hukumar zabe ta INEC da kada ta janye dan takararta daga rumfarta ko katin zabe gabanin zaben gwamna.
A wani labarin kuma, FG Ta Bada Umarnin Yin Bincike Kan Musabbabin Hadarin Jirgin Kasan Legas
Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ya umurci hukumar NSIB da ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan wani karo da wani jirgin kasan fasinja ya yi da wata motar safa da ke jigilar wasu ma’aikatan gwamnati zuwa wuraren aikinsu a Legas da safiyar Alhamis.
Da yake bayyana hatsarin a matsayin abin takaici, Sirika ya baiwa jama’a tabbacin cewa hukumar NSIB na iya zakulo musabbabin hatsarin nan take da nesa da kuma samar da hanyoyin dakile irin wannan a nan gaba.