Kotu ta tsare wani bisa zargin barazanar kashe mahaifiyarsa
Wata Kotun Majistare da ke Abakaliki a ranar Juma’a ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai shekaru 35, Monday Ikeagwu, a gidan gyaran hali bisa zarginsa da yin barazanar kashe mahaifiyarsa.
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Ikeagwu da laifin barazana ga rayuwa da kuma satar naira 625,000 mallakin mahaifiyarsa, Jacinta.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƴan sanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da fashi da makami a Kwara
Alkalin kotun, Lillian Ogodo, bai dauki karar Ikeagwu ba saboda rashin hukumci.
Ogodo ya ce ya kamata a mika fayil din karar da dukkan bayanan da aka gabatar ga ma’aikatar kararrakin jama’a domin samun shawarar lauya.
Ogodo ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga Maris.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Insp Chinagorom Eze, ya shaida wa kotun cewa Ikeagwu ya aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Fabrairu a unguwar Obodoma Ekka da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa a Ebonyi.
Eze ya ce Ikeagwu ya yi barazanar kashe mahaifiyarsa da bindiga.
Ya ce mutumin mai suna Ikeagwu ya kuma sace tsabar kudi N625,000 na mahaifiyarsa.
Eze ya ce Ikeagwu, ya aikata laifin da za a hukunta shi a karkashin sashe na 390 (9) na kundin laifuffuka, Cap. 33, Vol. 1 Dokokin Jihar Ebonyi, Najeriya, 2009.
Lauyan da ake kara, Solomon Eguji, ya roki kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa.
Eze, duk da haka, ya ki amincewa da neman belin
A wani labarin kuma:Bude iyakar Najeriya da Nijar: An umarci Ma’aikatan Hukumar Shige da fice da su koma bakin aiki
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ci gaba da inganta wutar lantarki da zuba jari a bangaren samar da wutar lantarki zai inganta wutar lantarki cikin watanni uku zuwa shida masu zuwa.
Mista Adelabu ya ba da wannan tabbacin ne a yayin ziyarar aiki da ya kai wasu ayyuka da ake gudanarwa a tashoshin Maryland da Alausa a ranar Alhamis a Legas.