Kotu ta umarci Kenye West da ya dunga baiwa tsohuwar matarsa Kim Kardashian Dalar Amurika dubu dari biyu duk wata a matsayin kudin ciyar da yarar da sulhu bayan rabuwar auren su. Kamar yadda BBC ta Ruwaito.
Tsohon Mawakin Rap da kuma Tauraruwar shirin shiryen Talbijin zasu raba dauyin dawainiyar kula da yayan su Hudu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tura Dalibin Da Ya Caccaki Aisha Buhari Gidan Yari
Kim Kardashian ta shigar da kara kan raba auren ta da tsohon mijin ta West da suka kawashe shekaru 8 a shekarara 202, wanda daga bisani ya sauya sunansa zuwa Ye.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan Kamfanoni da dama sun yanke alaka da Mr Ye.
A cikin watan Maris dukkannin su sun sanar da mutuwar auren su bayan Kardashia ta cire sunan sa wato “West” daga cikin jerin sunayen ta.
A jiya Talata ne kotu ta sulhubta samanin da ake samu tsakanin ma’auratan dangane da kula da yayansu.
Makudan kudaden da za a kashe wajan kula da tsaron yaron, Makarantansu, da dai sauransu, za a raba ne tsakanin ma’auratan.
Kazalika Ye, zai dunga buyan Dala Dubu dari biyu duk wata ga Kardashia saboda yaran za su fi kwashe lokaci mai tsayi suna tare da ita a Birnin New York
Tsofaffin Ma’auratan na da uara hudu Masu suna, North mai shekaru 9, Saint, Mai shekaru 6, Chicago mai shekaru hudu, da kuma Psaln mai shekaru 3
A wani labarin kuma, Sojoji Sun Kubutar Da Tsohuwa Yar Shekara 85 Da Wasu Mutane A Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Larabar da ta bayyana cewa, dakarun sojin Najeriya sun gano gawarwaki wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe su.
Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaron da kula da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya kuma tabbatar da cewa sojojin sun kwato wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga a dazuzzukan Chikun-Kachia-Kajuru.