Wata babbar kotun jihar Ondo ta yanke hukuncin kisa kan wani mutum mai suna Daniyan Ojo bayan samun sa da laifin hallaka matarsa.
Kotun ta ce ta kuma same shi da laifin cinnawa matar tasa wuta, bayan ya hallaka ta har lahira.
Mutumin mai shekaru 50, mai sana’ar walda, an same shi da laifin aikata laifin ne, yayin da ya kona gidansu tare da kulle matarsa a cikin wani daki a gidan tana barci.
An ce ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Satumba, 2019, a titin lrese dake kauyen Shagari a Akure, babban birnin jihar.
Bayan ya aikata laifin ne jami’an rundunar ‘yan sandan jihar suka kama shi, sannan suka gurfanar da shi a gaban kotu.
Lauyoyin masu shigar da kara da kuma wadanda ake tuhuma duka sun kasance a gaban kotu shekaru uku kafin daga bisani kotun ta yanke hukuncin.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Adegboyega Adebusoye, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da karar da ake yi wa Ojo ba tare da wata shakka ba kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.