Femi Falana, Babban Lauyan Najeriya, SAN, ya musanta ra’ayin da ake yi na cewa kotun daukaka kara ta tsige Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf daga mukaminsa.
Falana ya tabbatar da cewa kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da zaben Yusuf, inda ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke.
Karanta nanZaben Gwamnan Kano: Kotun Daukaka Kara ta Bukaci Dawo da Kwafin hukuncin da Aka Yanke Domin Gyara
Da yake magana a gidan talabijin na Arise News Primetime Show, Falana ya bayyana cewa ya nazarci Certified True Copy na hukuncin, inda ya nuna rashin jin dadinsa da sabanin da aka samu.
A cewar Falana, hukuncin da aka yi masu rinjaye ya yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke, inda ta yanke hukuncin da ya tabbatar da sahihancin Yusuf, sannan kuma ya amince da duk wani sassaucin da gwamnan ya nema.
Falana, ya kuma yi kira da a koma kan shawarwarin da kwamitin zaben mai shari’a Uwais ya bayar, ya kuma jaddada bukatar samar da mizani na bai daya don tabbatar da zabe ya yi daidai da ra’ayin jama’a.
A wani labarin kumaDa Dumi-Dumi: Gwamnan Kano Yusuf ya Garzaya Kotun Koli Kan Hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta Yanke
Lauyan ya kuma soki yadda ake dora mutane kan kura-kuran da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi, da jami’an hukumar, inda suka bukaci a kafa hukumar yaki da laifukan zabe mai zaman kanta.
Ya ba da shawarar cire hukumar zabe ta INEC domin mayar da hankali wajen gudanar da zabuka, tare da kafa wata hukumar ta daban kan laifukan zabe da kuma ka’idojin jam’iyyun siyasa.