By Abbas Yakubu yaura
Wata kotu a kudancin Libya a ranar Alhamis ta mayar da Seif al-Islam Gaddafi, dan marigayi Moamer Gaddafi, a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa da za a yi a wata mai zuwa, kamar yadda kafafen yada labarai na Libya suka ruwaito.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Seif al-Islam Gaddafi ya shigar da kara da safiyar yau a kotun dake Sebha kan kin amincewar da hukumar zabe ta yi na bukatarsa a matsayin dan takara a watan jiya.
Hukumar ta yi nuni da wasu batutuwa na dokar zabe dake nuna cewa “ba lallai ne a yanke wa ‘yan takara hukuncin daurin rai-da-rai ba” kuma dole ne su gabatar da cikakken tarihin aikata laifuka.