Gwamnan Jahar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sake jaddada buƙatar masu riƙe da maƙaman Shugabanci, dasu bada himma wajen neman Ilmin Addinin Musulunci, wanda a cewar sa hakan zai yi masu jagoranci akan yadda zasu gudanar da Kyakkyawan Shugabanci.
Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Shuwagabannin Hukumomin Gwamnati, da Manyan Sakatarori, da Jami’an ɓangaren Shari’a wanda suka samu jagorancin Babban Jojin Jahar Katsina Musa Danladi Abubakar domin ziyarar yi mashi Barka da Sallah a gidan Gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutumin Da Yasha Giya Yake Tiƙar Rawa Ba Jami’in Mu Bane – KAROTA
Alhaji Aminu Bello Masari ya nuna takaici akan ɗabi’un wasu masu riƙe da maƙaman Gwamnati duk da irin nauyin dake kansu na tabbatar da kyakkyawan aiki.
Gwamnan wanda ya tunatar dasu cewa a kowane lokaci Shugaban ci na zuwa da nauye-nauye, yace za’a tambaye su komai a ranar gobe Ƙiyama.
Ya yi amfani da damar wajen janyo hankalin su akan Babban zaɓen Shekarar 2023, sai ya buƙaci addu’a ga Jahar domin ta samu nagartaccen Shugaba wanda zaiyi fiye da abinda wannan Gwamnatin ke yi.
Tunda Farko, Shugaban tawagar, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar yace ziyarar nada manufar yi mashi Barka da sallah, bayan samun nasarar kammala Azumin Watan Ramadan.
Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya bada tabbacin cewa irin abubuwan da suka koya, da halartar Tafsiri, da kuma addu’o’in da suka yi, zai taimaka masu matuƙa wajen sake yin ƙwazo ga ayyukan su.
Babba Jojin ya yabawa Gwamnan daya basu damar gudanar da aikin su yanda ya kamata, yasha alwashin cigaba taimakon juna domin samar da Kyakkyawan Shugabanci a Jahar.
Shugaban Majalisar Dokokin Alhaji Tasiu Musa Maigari, da Grand Khadi na Jahar Dr Mohd Kabir, da Muƙaddashin Sakataren Gwamnati Alhaji Muntari Lawal, sa Shugaban Ma’aikata na Jaha Alhaji Idris Usman Tune na ɗaya daga cikin manyan mutanen da suka halarci wannan taro na ban girma na Sallah.