Wani jigo a jam’iyyar PDP, Umar Sani, ya shawarci jam’iyyar adawar da ta dakatar da Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, saboda ayyukan da suka yi na cin amana a yayin babban zaben da aka kammala, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Sani, wanda tsohon mai baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Namadi Sambo ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata hira da gidan talabijin na Arise da jaridar DAILY POST ta sanyawa ido.
KARANTA WANNAN LABARIN: Baɗakalar N1bn: EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Shugaban Jami’ar ABU da Bursar
A cewarsa, ya kamata a dauki Wike kamar tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Pius Anyim da sauran wadanda jam’iyyar ta dakatar a makon jiya.
Ya bayyana cewa Wike, wanda shi ne majagaba na Gwamnonin G5, shine babbar matsala ga jam’iyyar.
Ya yi tambaya: “Wane ne mafi adawa da Gwamna Nyesom Wike, mutumin da ke zagin Shugaban jam’iyyar, dan takarar shugaban kasa kullum?”
Rikicin da ya biyo bayan zaben ya ci gaba da ruruwa a jam’iyyar PDP, lamarin da ya kai ga tsige shugaban jam’iyyar Sanata Iyorcia Ayu.
A wani labarin kuma, Jirgaen Sojoji Biyu Sun Gamu da Hatsari, Mutane da Yawa Sun Mutu
Wasu jirage masu saukar ungulu na sojojin Amurka biyu na Black Hawk sun fado a jihar Kentucky a yayin wani atisayen da suke yi a daren Laraba, lamarin da ya yi sanadin “mummunan hasarar rayuka,” in ji jami’ai.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa, jiragen sama masu saukar ungulu daga runduna ta 101 ta Airborne (Air Assault) sun yi hatsari da misalin karfe 10 na daren Laraba a gundumar Trigg ta Kentucky dake arewa maso yammacin Fort Campbell.