Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya NSCIA ta ce kona Alkur’ani mai girma da aka yi a birnin Stockholm na kasar Sweden
Wani lamari ne na tunzura jama’a da kuma cin zarafi da ke tabbatar da yawaitar kyamar Musulunci a tsakanin wasu mutane a duniya kamar yada jaridar Premium Times ta bayyana
A wata sanarwa da Salisu Shehu mataimakin babban sakataren majalisar ya fitar, ya ce wannan matakin shaida ne na rashin hukunta wasu masu kiyayya ga musulmi
Malam Salihu ya ce mutumin da ya wulakanta Alkur’ani mai girma bai damu da tunanin biliyoyin Musulmi a duniya ba
Ya bayyana mamakinsa cewa ta yaya za a yarda ayi irin wannan aiki a kasar da aka yi biki a matsayin kasa mafi zaman lafiya a duniya
Abin mamaki ne a ce za a kyale wani aikin sabo a halin yanzu a kasar da ake yawan yin bikin a matsayin daya daga cikin mafi zaman lafiya a Turai baki daya
Majalisar ta yi matukar kaduwa da cewa yan sandan Sweden masu hankali da wayewa ba za su iya kama wanda yayi wannan danyen aiki ba,inda suka bar shi ya tsira ba tare da Wani hukunci ba
Mista Salihu ya zargi kasar Sweden da sauran kasashe da kyale tare da goyon bayan wulakanta alamomin addinin Musulunci ba tare da la’akari da illar irin wadannan ayyuka ba
KARANTA NANGwamnatin Jahar Katsina Zata Dauki Matasa 2400 Aiki Don Magance Matsalar Tsaro A Jahar
Ya ce irin wadannan kasashe sun lalata kimarsu a matsayin kasashe masu wayewa yayin da Musulmai za su dauki shelarsu ta kare hakkin dan Adam da DIMOKURADIYYA a matsayin wata farfaganda
Yayin da Mista Salihu ya ce NSCIA ta yi imanin cewa babu wani littafi mai tsarki da za a tozarta, Majalisar ta yi kira ga hukumomin Sweden da su yi bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
Majalisar ta yi kira ga Hukumomin Sweden da su gaggauta yin bincike kan lamarin, su bayyana rahoton a bainar jama’a
A WANI LABARIN KUMA‘Yan sanda Sun Dakile Wani Yunkurin Satar Man Fetur A NNPC
Kuma su tabbatar da cewa ba wai kawai an yi adalci ba,A halin da ake ciki, Majalisar ta umurci al’ummah a fadin duniya da su kwantar da hankulansu kuma su ci gaba da zaman lafiya da bin doka da oda a tunkarar wannan tada zaune tsaye