Zaman ɗar-ɗar da tsoro na cigaba da ƙaruwa a Ukraniya akan yaƙin Sojoji da Rasha ta ƙaddamar, Ofishin Jakadancin Najeriya dake Ukraniya ya shaidawa ƴan Najeriya mazauna Ƙasar dasu kare kansu.
Ƴan Najeriya da dama dai sun faɗa tarko a faɗan, wanda har yanzu Shuwagabannin Duniya sun kasa shawo kan matsalar, duk da gargaɗi, da kulle su gami da roƙo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gbajabiamila Ya Bada Umarnin Kwaso Daliban Najeriya Daga Kasar Ukraine Cikin Gaggawa
Ofishin Jakadancin Najeriya ya bayyana haka a wani saƙon bayar da shawara, daya gabatar jim kaɗan kafin Rasha ta Ƙaddamar da hari a Ukraniya.
Shawarar dai kuma maida martani ne akan ayyana Dokar ta ɓaci gaba ɗaya Ukraniya, sai dai banda yankin Donetsk da Luhansk.
Ofishin Jakadancin Najeriya yayi kira ga ƴan Najeriya dasu zama masu haƙuri, su kuma kula da tsaron su da lafiyar su.
“Ofishin Jakadancin ya kuma shawarci ƴan Najeriya dasu nemi mafaka a wuraren da kuke ganin zaku ɓoye. Kuma kuyi duk abinda zaku yi domin gyara dukkanin takardun ku, don dawo a Ƙasar
Comments 1