Ku Saki Bawa – Falana Ga DSS
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana ya bukaci a sako shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa da ke tsare.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa a halin yanzu Bawa na tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) dake Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN:Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS ta Yi Fatali da Shirin Mika Mulki Na Tchiani
Bawa, wanda ya kasance a hannun DSS na tsawon kwanaki 67 tun daga ranar 14 ga watan Yunin 2023, ana tuhumarsa da laifin almundahanar kudi a karkashin kulawar sa.
Sai dai Falana, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Legas, ya ce umarnin tsare Bawa ya kare, yana mai cewa hukumar DSS ba ta da hujjar ci gaba da tsare shi.
Sanarwar a wani bangare na cewa: “Duba da yadda ba a tuhumi Mista Abdulrasheed Bawa da wani laifi ko kadan, ya kamata hukumar tsaro ta farin kaya ta sako shi daga tsare. Ba ni da masaniya game da ikirarin cewa ana tsare da Mista Bawa ne bisa umarnin tsare shi da wata kotun majistare da ke babban birnin tarayya ta bayar.
“Ya kamata a nuna cewa umarnin tsare mutane ya zama abin kashewa, ba shi da amfani, kuma ba bisa ka’ida ba, domin babu wani alkali da ke da iko a karkashin sashe na 493 na dokar hukunta manyan laifuka ta 2015, ko kuma sashe na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya na bayar da izinin tsare shi wanda ake zargi da aikata laifuka na tsawon kwanaki 67 ba tare da shari’a ba.
A wani labarin kuma:Tinubu ya sauya mukaman wasu ministoci da ya nada kwanannan
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta ce ba za ta amince da shirin mika mulki ga gwamnatin mulkin sojan Nijar na tsawon shekaru uku ba.
Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musa ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wata hira da BBC.