Ministan tsaro, Alhaji Mohammed Badaru, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’o’in kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Badaru ya yi wannan kiran ne ranar Alhamis a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin tawagar yan asalin jahar Jigawa karkashin jagorancin gwamnan jihar, Malam Umar Namadi.
Ya ce tare da sarkakiyar kalubalen tsaro da sauran abubuwan da suka shafi ci gaban kasa ya kamata a dinga yin addu’oi don samun nasara.
KARANTA NANBa Zamu Taba Yin Kasa A Gwuiwa A Yaki Da Yan Ta’adda Ba-Gwamna Radda
Ministan tsaron, ya ce duk da cewa aikin da ke gabansu na da yawa, amma sun kuduri aniyar shawo kan kalubalen.
Don haka Badaru ya tashi tsaye wajen neman goyon bayan daukacin ‘yan Najeriya ciki har da addu’o’insu domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Tun da farko gwamnan jihar Jigawa wanda ya jagoranci sarakunan gargajiya da malaman addini da ‘yan kasuwa da masu rike da mukaman gwamnati daga jihar ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya ministan murna tare da ba shi tabbacin goyon bayansu a kowane lokaci.
Ba wai don taya murna ba ne, har ma a yi muku addu’a. Mun san yadda ka yi nasara a matsayinka na gwamnan jiharmu, muna kuma yi maka addu’ar samun nasara ko ma fiye da haka a wannan sabon aikin na Ministan Tsaro.
A WANI LABARIN KUMAKotu Ta Daure Lebura Akan Laifin Satar Karfen Rodi A Abuja
Namadi ya tunatar da ministan cewa ’yan Najeriya na da kyakkyawan fata cewa zai yi wa kasa hidima tare da magance matsalar rashin tsaro a kasar, inda ya kara da cewa “da zarar ka iya yin hakan, ya shafi kowane bangare na kasa.
Namadi ya kara da cewa mun yi sa’a muna zaman lafiya a Jigawa, amma hakan ba yana nufin ba ma bukatar taimakon ku, muna kuma bukatar taimakon ku kamar yadda kuke taimakon sauran jihohin.