Ku Yi Watsi Da Labaran Karya Kan Cewa Mun Kashe Sojoji Inyamurai –Rundunar Soji
Rundunar sojin Nijeriya ta nemi al’umma da su yi watsin jita-jitar da wadansu gamayyar kungiyoyi ke yadawa cewa rundunar na gudanar da shari’ar sirri tare da kashe sojoji Inyamurai guda shida.
Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dai a ranar Talata ne suka yi wannan zargin. Sai dai rundunar sojin ta ce ba gaskiya a lamarin.
Rundunar sojin ta bayyana hakan ne a shafinta na sada zumunta, inda ta bayyana labarin a matsayin labarin karya domin batawa rundunar suna.
Wani babban jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi watsi da zargin, inda ya ce ba abu ne mai yiwuwa a ce rundunar sojin na gudanar da shari’ar sirri ba ga kowanne soja ma.
Ya yi karin haske da cewa; a koyaushe sojojin shari’o’insu a bayyane ake yi a kuma gaban jama’a ga duk wani soja da ake zargi, inda ya ce kuma wadannan kotun suna da shugaba da membobi. Inda ya ce shari’ar a bayyane ake yi ba a boye ba.
“babu gaskiya cewa an yiwa sojoji shida shari’a a sirrance tare da kashe su a ranar 25 ga watan Janairu . Wadanda suke yada hakan makiyan Nijeriya ne, wadanda suke neman haddasa rikicin kabilanci a kasarnan”. Ya tabbatar.