Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a ranar Alhamis, ya ce tun lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabon umarninsa kan sabuwar manufar Naira, ya gana da shugabannin wasu bankunan kasuwanci kusan 15.
CBN ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci fadar shugaban kasa sa’o’i bayan watsa shirye-shiryen talabijin a fadin kasar inda ya bayyana cewa tsohuwar takardar kudi ta N200 ce kawai za ta ci gaba da zama a kan doka har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matar Tinubu: Mutane Sun Ce Mu Masu Kudi Ne, Ko Ajiya Sai da Na Roki Naira Miliyan N2m
Ya ce ganawar da shugabannin bankunan a ranar Alhamis ta zone don tabbatar da wadatar da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 domin rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki.
A wani labarin kuma, Karancin Kudi: Zulum Ya Umarci Asibitocin Gwamnati Su Raba Maganguna Kyauta
Gwamna Babagana Zulum na Borno ya bayar da umarnin a fitar da magungunan da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 da sauran kayayyakin jinya zuwa asibitocin gwamnati domin rabawa marasa lafiya kyauta wadanda akasarinsu ke fuskantar matsalar biyan kudi sakamakon karancin kudi na sabbi da tsoffi na Naira.
Kwamishinan lafiya da aiyukan jama’a Farfesa Mohammed Arab ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da magungunan a Maiduguri.
Arab ya ce kayayyakin sun hada da magunguna na cututtuka masu yaduwa, kayan haihuwa da sauran kayan masarufi.
Kwamishinan ya umurci daraktocin kiwon lafiya da manyan jami’an kiwon lafiya na cibiyoyin kula da lafiya na jama’a da ke Maiduguri Metropolitan Council da karamar hukumar Jere da su shirya takardun aiki don karbar kasonsu domin a gaggauta tura magungunan da sauran kayayyaki.