Raveran Father Mathew Hassan Kukah na cocin Katolika yace duk da irin Caccakar daya ke yiwa Gwamnatin Buhari, amma Shugaban Ƙasar bai daina ɗaukar wayar sa ba.
Shehin Malamin Addinin Kirista, wanda yayi ƙaurin suna wajen caccakar Gwamnatin yanzu a taruka da dama, yana ƙalubalantar Gwamnati akan ɓangaranci.
Dayake jawabi a sakatariyar Cocin dake Sokoto a ranar Juma’a, Kukah yace yana da dangantaka da Shugaban Ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar PDP Zamfara Ta Sha Alwashin Neman Adalci Akan Harin Da Wasu Ƴan Baranda Suka Kai
Kukah ya ƙara da cewa irin damuwar da yake yi ba rashin tsaro, da kisa a Ƙasar, shine ya haddasa wannan Caccakar bawai tsanar Gwamnatin ba.
“Idan na ɗauki waya na kira Shugaban Ƙasa a yanzu, zai ɗaga mata. Lokacin da ya rasa kira na, sai da ya kirani daga baya, muka gaisa da juna.
Kukah ya goyi bayan Shugaban Ƙasa na ƙin sanya hannu a dokar zabe, yana mai cewa ya kamata a baiwa jam’iyya damar zaɓar ɗan takarar da take so a zaɓe