A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci hafsoshin tsaron kasar nan da su tabbatar da cewa an samu gagarumar nasara kan dimbin barazanar tsaro da ke addabar kasar.
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a lokacin da yake jawabi ga hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin leken asiri a lokacin taron tsaro na shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Karanta nanBabu Hannuna A Badakalar Naira Biliyan 37-Beta Edu
Ya ce yayin da ake samun ci gaba mai kyau tare da kawar da wasu matsalolin tsaro a cikin gida da yawa,a wasu wuraren kuma ana samun karin hare haren yan bindiga.
A cewarsa ba na wasa da rahotannin sirri na. Ina da layukan gani da yawa. Dole ne rassan sojojin ruwa su kara kaimi domin cimma burinmu na amfanin dukkan ‘yan Nijeriya.
Kuna matukar kokari kuma yan Nijeriya suna gani amma dolene a kaucewa faruwar kuskure kamar wanda ya faru a Kaduna kwanan nan inji Tinubu.
Na ji dadin yadda hadin kai tsakanin dukkan hukumomi ya samu ci gaba sosai a cikin ‘yan watannin nan, amma bazamu yi murna ba har sai mun kawo karshen wannan matsalar dake addabar mu inji shugaban.
A wani labarin kumaKada Ku Bari Kabilanci Ya Raba Kawunanku-Muftwang Ga Al’ummar Filato
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dole ne sojojin kasar su cimma burinsa na ganin kasar nan ta samu dawwamammen zaman lafiya inda za a samar da ganga miliyan biyu na danyen mai a kowace rana a cikin rubu’in farko na shekarar 2024.
Shugaban kasar ya yi wa sabbin hafsoshin da aka yi wa karin girma ado wanda babban hafsan hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar ya taimaka masa; babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja; da Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, a gaban matan manyan jami’an.
Taron ya samu halartan mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu; Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle; Shugabannin Ma’aikata; Shugabannin hukumomin leken asiri, da kuma mataimakan shugaban kasa.