Wani babban Fasto kuma mabiyin akidar Anglican dake wata Coci a Enugu ya bukaci Majalisar Dattawa da ta wakilai da ta kirkiro da dokar da zata hana a rantsar da shugaban da ya lashe zabe
Har sai bayan an kammala shari’ar da aka shigar ta kalubalantar nasararsa a kotu,inda ya kara da cewa hakan zai rage jinkirin da sabon shugaba zai yi kafin ya fara gudanar da aikinsa
Faston kamar yada jaridar Vanguard ta ruwaito yana cewa kamata yayi ace duk lokacin da aka kammala zabe to kada a kuskura a rantsar da wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zabe
KARANTA NANGwamnan Kano Ya Gwangwaje Alhazai Sama da Dubu 6 Da Kyautar Makudan Kudade
Har sai bayan an kammala shari’a dashi a kotun zabe ta Najeriya idan har ta tabbata shi ya lashe zabe shikenan sai a rantsar dashi idan kuma ba shi ya lashe zabe ba baza a rantsar da shiba
Faston ya kuma yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu akan matakin da yake dauka wajen dawo da martabar Najeriya musamman sauya tsofaffin manyan Hafsoshin Tsaron Kasar da yayi
Inda ya bukaci mabiyansa da su saka Bola Ahmed Tinubu a cikin addu’o’insu don ganin ya kammala mulkinsa lafiya ba tare da wata matsalar ba
A WANI LABARIN KUMA
Akwai Babban Aiki A Gabanku-Tinubu Ga Hafsoshin Tsaro
Bayan ganawar sirri da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da sabbin manyan Hafsoshin Tsaro na Najeriya, ya tabbatar masu da cewa akwai babban aiki a gabansu don haka su dage wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin tarayyar Najeriya
Shugaba Tinubu ya kara tabbatar masu da aniyarsa ta cika alkawarin da ya dauka a lokacin Yakin neman zabe,na tsare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya