Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta amince da mayar da Kwalejin Noma da Kimiyyar Dabbobi ta Bakura zuwa Kwalejin Noma da Fasaha yayin da aka kammala shirye-shiryen gyara ta.
Kwamishinan noma na jihar Ya’u Haruna Gamji ne ya bayyana hakan bayan kare kasafin kudin ma’aikatar na shekarar 2024 a gaban kwamitin riko na majalisar dokoki kan kasafin kudi.
Karanta nanAddu’a Ce Kawai Zata Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamafara-Sanata Yari
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Bashir Abashiya ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa,Kwamishinan ya ce an inganta kwalejin ne domin a dunkule kan burin tsohon Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello wanda ya kafa cibiyar domin samar da matsakaitan ma’aikata don ayyukan fadada ayyukan noma a yankin.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan ingantawa zai kuma baiwa kwalejin damar cin gajiyar Tetfund da sauran ayyukan bada tallafi ta hanyar inganta ababen more rayuwa da inganta iya aiki ga ma’aikatan cibiyar.
A wani labarin kumaDole Ne Mu Hada Kai Don Tabbatar Da Zaman Lafiya a Najeriya — Tinubu Ga gwamnoni
Hakazalika Ya u Haruna ya ce gwamnatin jihar ta amince da sake amincewa da kwasa-kwasan da ake da su da kuma amincewa da kwasa-kwasan da hukumar ke shirin bullo da su a matsayin wani sharadi na sauya shekar kwalejin daga Monotechnic zuwa Polytechnic kamar yadda hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa ta bukata.
Hakan zai kara yawan makarantun Polytechnic da jahar keda su da suka hada ta Abdu Gusau Polytechnic da kuma Federal Polytechnic Kauran Namoda.