Wani dattijo mai shekaru 78 yana neman a dawo masa da kudin sadakin da ya biya ya yin auren su da matarsa bayan ya gano cewa dansa mai shekaru 49 ba nasa ba ne.
Wilson Shirichena daga Mhondoro ta kasar Zimbabwe wanda aka kai ga yarda cewa Milton Shirichena ɗansa ne na cikin sa shekaru arba’in da suka gabata, har yanzu yana cikin kaduwa bayan gano abin mamaki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za A Mayar Da Otal Din Da Messi Ya Zauna A Qatar Zuwa Gidan Tarihi
Kafofin yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa Wilson ya yi zargin cewa “ɗansa” Milton ya samu ziyara daga mahaifinsa na gaske, wanda ya gaya masa cewa ɗansa ne kafin ya mutu. Yanzu yana neman Milton ya dawo masa kudin sadakin tunda iyayen matarsa wato surukansa sun mutu.
Wilson ya ce;
“Lokacin da aka gaya min haka, na yi baƙin ciki sosai da na gano cewa matata ƙaunatacciya za ta ɓoye mini wannan har tsawon shekaru 43.”
“Yanzu ina neman a dawo mini da kuɗin lobola wato sadaki daga Milton tun da na biya diyya wanda ya kamata mahaifinsa ya biya, wanda ya yi wa matata ciki kafin mu yi aure.”
“Matata ba ta jin daɗi. Tana da tabin hankali, kuma duk surukaina sun mutu. Don haka Milton ya kamata ya biyani kuɗina na sadaki a madadin mahaifinsa.”
Milton ya musanta zargin cewa ya yi magana da “mahaifinsa na haihuwa” lokacin da yake raye.
Yace;
“Ba zan iya musanta cewa akwai jita-jita da ake ta yadawa cewa ni ba dan Wilson ba ne, amma ba mu taba yin magana a kai ba, idan yana da hujjar abin da yake fada, to ya bi hanyoyin da suka dace da ya kamata a yi fiye da korafe-korafe. ni daga dangi kamar kare.”
A wani labarin kuma,
A wani labarin kuma, Farashin Zinari Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Masar
Farsashin Zinari yayi tashin gauran zabi a ƙasar Masar, a dai dai lokacin da mahukunta ke neman mafita akan rashin tasirin kuɗaɗen ƙasar, yayin da kamfuna ke fitar da kayayyakin domin daƙile karamcin Dalar da ake fama da shi, domin samun kudaden da zasu shigo da kayyaki Kamar yadda masana ɓangare masana’antu suka bayyana. Kamar yadda Reuters ya ruwaito.
Alƙalumma daga hukumar hada hadar kasuwanci ta kasar Masar Bangaren Zinari, (FEDCOC) sun nuna cewa farshin zinari Nauyin Gram 1, ya zarce Dalar Amurka dubu daya da dari takwas a watan Disamban nan, farashin da kafafaen yaɗa labarai ƙasar sukace shi ne mafi girma tsawon lokaci.