Kwamitin NUC ya bankado wasu sirrika na wasu Jami’o’i biyu a Arewa
Kwamitin da tsohon babban sakataren hukumar kula da jami’o’i ta kasa Farfesa Abubakar Rasheed ya kafa domin duba ayyukan jami’o’i masu zaman kansu guda biyu a kasar ya mika rahotonsa ga hukumar, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.
Jami’o’in sun hada da Jami’ar Ave Maria, Piyanko, Jihar Nasarawa, da Jami’ar Khadija, Majia, Jihar Jigawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Mai Mallakin Twitter Ya Yi Wani Tsokaci Kan Bude Shafin Threads
Wakilinmu ya gano cewa rahoton da aka gabatar bayan shafe watanni biyu ana zaman, ya gano cewa daya daga cikin jami’o’in na da shugaban jami’ar na wucin gadi yayin da daya kuma tana da shugaban tsangaya na wucin gadi.
Hukumar ta NUC ta kafa kwamitin ne karkashin jagorancin Farfesa Francis Egbokhare, tare da dora shi alhakin duba ayyukan jami’o’in, bisa lura da cewa ba sa bin dokokin da ke tafiyar da su.
Hukumar ta NUC ta ce rahotanni sun nuna cewa masu hannun jarin na yin katsalandan a harkokin tafiyar da Jami’o’in.
A cewar rahoton, wanda wakilinmu ya gani, mataimakin shugaban kwamitin, Farfesa Yahuza Bello, wanda ya wakilci shugaban, ya ce kwamitin ya lura da dimbin al’amurra a Jami’o’in biyu, “daga yadda aka lura da yadda ake gudanar da ayyukansu da kuma yadda ake tafiyar da su.”
Sai dai kwamitin ya bayar da shawarwari, wadanda ta ce za su amfani jami’o’in da abin ya shafa da ma sauran sassan kasar nan.
A wani labarin kuma:Tsohon Mai Mallakin Twitter Ya Yi Wani Tsokaci Kan Bude Shafin Threads
Shugaban kasar Bola Tinubu a ranar Juma’a a Abuja, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta gano tare da kawar da cikas don sanya tattalin arzikin Najeriya ya habaka wajen kara zuba jari.
Ya ce za a yi gyare-gyaren tattalin arzikin ne domin baiwa matasan Najeriya fifiko.