Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Laraba ya bukaci al’ummar jihar Delta da su marawa jam’iyyar baya tare da kada mata kuri’a a zaben 2023 mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ruwaito.
Kwankwaso ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da ofishin yakin neman zaben Honorobul Onochie Anthony Ochie a garin Ogwashi-Uku, dake Jihar Delta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Aike Da Wani Matashi Gidan Yari, Bayan Ya Haikewa Karamin Yaro
Ya ce jam’iyyar NNPP jam’iyya ce ta kasa da za ta iya doke kowace jam’iya a fadin Najeriya.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan takarar jam’iyyar NNPP da su dukufa wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben.
Kwakwaso ya yi alkawarin gina ajujuwa 500 a cikin shekaru uku, tare da fitar da yara kan tituna da kuma samar da dimbin ayyukan yi ga jama’a.
Tun da farko, Dan Takarar Majalisar Wakilai ta NNPP mai wakiltar mazabar tarayya ta Aniocha/Oshimili, Honorabul Onochie Anthony Ochie ya tarbi Kwankwaso zuwa Ogwashi-Uku domin kaddamar da ofishin yakin neman zabensa.
A wani labari kuma, Wani Kwamishinan Yan Sanda Ya Ja Kunnen Sabbin Jami’an Rundunar
A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta karbi sabbin ‘yan sandan da suka kammala karɓar horo daga makarantar horas da ‘yan sanda ta PTS Sokoto da aka turo su jihar nan.
Da yake jawabi ga sabbin jami’an ‘yan sandan guda 262 a hedkwatar rundunar da ke Birnin Kebbi, kwamishinan ‘yan sandan jiha Ahmed Magaji Kontagora ya taya sabbin jami’an murna, tare da jan hankalinsu da su kasance masu ɗa ‘a da nuna kwarewa yayin gudanar da aikinsu.
Ya kuma yi kira gare su da su nisanta kan su da tafiye-tafiye da dare, tare da kaurace sanya kakin su yayin da za su yi tafiya.
Hajiya Fatima Abubakar, ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar ADC a Borno, ta ce tana da kwarin gwiwar doke Gwamna Babagana Zulum, dan takarar jam’iyyar APC a zaben Mach 11. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.