Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce kasashen Afrika bakwai ne kawo yanzu aka tabbatar da samun rahoton bullar cutar Kyandar biri guda 1,400 a cikin Annan shekarar..
Wadannan nadaga cikin adadin 1,392 da Ake Zargi sun kamu da cutar, da kuma 44 wadanda aka tabbatar sun harbu.
Wadanda aka samu sun kamu da cutar sun fito ne daga kasashen Kamaru, Afrika ta tsakiya, Jamhoriyar Dimokuradiyyar Congo, Liberiya, Najeriya, Congo-Brazzaville da kuma Saliyo.
A cewar hukumar WHO adadin da kasamu a wannan shekarar yayi kasa da Wanda akasamu a shekarar da ta gabata.
Kazalika Babban darakatan hukumar a yankin nahiyar Afrika Dr Mat-shu-di-so Moeti ya bukaci hukumomin kasashen Afrika da su farga wajan ganin sun dakile yaduwar cutar a tsakanin al’uma.