By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a ranar Lahadi ya jagoranci iyalansa zuwa jihar Imo, yayin da aka yi jana’izar matarsa ta farko, Hajiya Zainab Marwa a Owerri.
Zainab ‘yar asalin Imo ta kasance kanwa ga tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA a jihar Imo, Cif Martin Agbaso.
Zainab Marwa ta rasu ne a ranar 8 ga watan Janairu, 2022, tana da shekaru 66 bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa jana’izar ta samu halartar manyan mutane daga sassa daban daban na cikin kasar nan.
Sauran karin bayanin suna cikin hotuna wurin jana’izar