Gwamnatin jihar Legas ta karkatar da zirga-zirgar ababen hawa daga babbar hanyar Epe/Ijebu zuwa Ode na Abeokuta daga karfe 7:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar Alhamis bayan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar Ogun.
Shugaban ya je jihar Ogun ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta fara aiwatarwa.
Kwamishinan Sufuri, Dr Frederic Oladeinde ne, ya bada tabbacin cewa an tsare wasu hanyoyin daban tare da tura jami’an kiyaye hadurra na tarayya da hadin gwiwar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun (TRACE) domin tabbatar da da zirga-zirgar ababen hawa bisa bin tsarin doka
Ya bayyana cewa ana sa ran masu ababen hawa da suka taso daga Legas Zuwa Abeokuta za su yi amfani da titin Legas Zuwa Sango/Abeokuta da Mowe-Ofada-Papalanto-Abeokuta ko kuma su yi amfani da hanyar Ijebu zuwaOde, Omu-Ketu, Epe don isa inda suke so.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa an zabo jami’an kula da ababen hawa daga jihohin biyu domin gudanar da aikin tabbatar da bin Dokokin hanya yayin zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyoyin da aka ambata.