Tawagar tallafawa Majalisar Dinkin Duniya a Libya UNSMIL ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa akalla bakin haure 15 da masu neman mafaka a birnin Sabratha dake yammacin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, tare da yin kira da a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
A ranar Juma’a ne aka gano gawarwakin bakin haure 15, wasu daga cikinsu sun kone a gabar tekun Sabratha kilomita 70 daga Tripoli babban birnin kasar, wani muhimmin wurin tashi ga dubban mutanen da ke neman isa gabar tekun Italiya a kowace shekara.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sandan Kaduna Sun Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne Da Masu Samar Da Makamai
“An gano gawarwakin mutane 11 da suka kone a cikin wani jirgin ruwa da aka makare sannan an gano wasu gawarwaki hudu da suka samu raunuka a waje,” inji Manul.
“Duk da cewa har yanzu ba a tantance hakikanin lamarin ba, amma ana kyautata zaton cewa kisan ya biyo bayan artabu ne tsakanin masu fataucin Bil’adama da masu adawa da juna,” in ji MDD, wadda ta bukaci mahukuntan Libya da su tabbatar da gudanar da bincike cikin gaggawa, mai zaman kansa da kuma gaskiya, domin kawo dukkan masu aikata laifin.
Wannan bala’i “abin tunatarwa ne sosai kan rashin kariya da bakin haure da masu neman mafaka ke fuskanta a Libya, da kuma cin zarafin bil-Adama da ake tafkawa ta hanyar safarar mutane masu karfi da masu aikata laifuka,” in ji tawagar MDD.
A cewar kafofin yada labaran kasar, an kashe bakin hauren wadanda akasarinsu daga yankin kudu da hamadar sahara suke ne a ranar Alhamis ta hanyar harbin bindiga biyo bayan takaddamar da ta barke tsakanin masu fasa kwaurin.
Daya daga cikin gungun ‘yan fasa kwabrin da rikicin ya rutsa da su ya kona jirgin a ranar Juma’a, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Rikicin da ya biyo bayan faduwar gwamnatin Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, ya sanya kasar Libya ta zama hanyar da aka fi so ga dubun dubatar bakin haure daga kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara, da kasashen Larabawa da kuma kudancin Asiya, masu kwadayin shiga Turai ta Italiya.
Wadannan bakin hauren na fadawa hannun masu fataucin mutane ne a lokacin da ba su mutu ba a yunkurin tsallakawa zuwa tekun Mediterrenean mai hatsarin gaske, kuma a kai a kai ana sukar Libya daga kungiyoyi masu zaman kansu saboda musgunawa da suke fuskanta.
Gwamnatoci biyu da ke samun goyon bayan wasu sansanoni biyu masu adawa da juna a yammaci da gabashin Libya sun fara fafatawa a kan karagar mulki tun watan Maris.
Tun daga farkon shekarar nan, an kame bakin haure 14,157 tare da mayar da su Libya, a cewar wani rahoto da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) ta fitar a ranar Litinin. Akalla mutane 216 ne suka mutu a yunkurin tsallakawa tekun Mediterrenean, yayin da wasu 724 suka bace kuma ana kyautata zaton sun mutu, a cewar hukumar ta IOM.
A wani labarin kuma, Jirgin Ruwana Da Ya Kife Yana Dauke Da Fasinjoji 48 Ne Ba 85 Ba” – Direba
Direban kwale-kwalen da ya kife a Ogbaru da ke Anambra a ranar Juma’ar da ta gabata, Mista Desmond Amugo, ya ce yana da fasinjoji 48 ba fasinjoji 85 ba kamar yadda ake ta yadawa.
Amugo ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin nan a Atani, shedkwatar karamar hukumar Ogbaru a lokacin da yake zantawa da jami’an gwamnati kan lamarin da ya haddasa hadarin.