Ƙungiyar likitoci ta Nijeriya, NARD ta yi barazanar tsunduma cikin yajin aiki a baki daya kasar daga ranar Alhamis, 1 ga Afrilu matukar ba a biya musu buƙatunsu ba.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen taronta na majalisar ƙoli, shugaban ƙungiyar Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi ya zayyano buƙatun na su wanda ya haɗa da biyan albashin da suke bi nan take da suka haɗa da na watan Maris wanda ya ce a biya su kafin 31 ga Maris din.
A cewarsa: “Buƙatun sun ƙunshi biyan dukkan albashin da muke bi bashi ga mambobinmu na asibitocin gwamnatin tarayya da kuma na makarantun kiwon lafiya na jihohi.
“A ƙara mana yawan alawus na afkuwar bala’i zuwa kashi 50 cikin 100 na albashin ma’aikata, sannan a biya alawus na aikin annobar korona musamman a cibiyoyin lafiya na jihohi.”
Kazalika, ƙungiyar ta nemi a kori rajistira na ƙungiyar Medical and Dental Council of Nigeria (MDCN) “saboda gazawarsa wajen gudanar da alawus-alawus na wasu likitoci”.