By Ishaq Dabai
Mutane uku dake aiki a wurin wani gini sun makale a karkashin tarkacen wani bene mai hawa biyu da ya rufta a yankin Ikorodu dake Legas ranar Litinin da daddare.Gidan, wanda ake kan ginawa, ya rushe a daren Litinin a tashar motar Haruna dake Ikorodu.
Mai sanya ido na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace masu ceto daga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), ’Yan sanda da Hukumar Kashe Gobara na neman mutanen da suka makale.
A cewar sa “Wani bene mai hawa biyu ya rushe a Ikorodu Haruna a kusa da wurin tsayawar a baben hawa kusa da bankin access dake Ikorodu,” in ji shi, faruwa lamarin keda wuya “mazauna yankin suka hada kansu don gudanar da ayyukan ceto na farko.
“Kodayake, hukumar kashe gobara da ‘yan sanda sun amsa amma sun kasa yin abin da yawa saboda rashin kayan aiki don tayar da jita -jitar a inda ake zargin wadanda abin ya rutsa da su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “tunda farko ginin da an yi watsi da shi ne masu gidan suka bukaci mazauna gidan dasu tashi suka ci gaba da zama a wurin ba tare da izinin mai gidan ba.”
Kazalika yace mutane biyu sunjikkata, namiji da mace, yanzu haka suna karbar magani a babban asibitin Ikorodu.sai dai kuma har zuwa yanzu aikin ceton wadanda abin ya rutsa dasu yana ci gaba da gudana har zuwa lokacin hada wannan rahoton.