Ma’aikatan gwamnatin a babban birnin tarayya Abuja, na ci gaba da kokawa kan yadda farashin man Fetur ke ci gaba da karuwa.
A cewar ma’aikatan yawancin Albashin su na tafiya ne ga Siyen man fetur, maimakon samun kayan amfani na yau da kullum.
KARANTA ANAN: Kadarorin Da FG Ta Kwato Ya Kamata Su Koma Ga Jihohi Kai Tsaye – CISLAC
A yayin zantarwar wasu dake kan layin shan mai a birnin Abuja da manema labarai, sun ce ya kamata gwamnatin tarayya ta kawo karshen wannan matsala cikin gaggawa domin su samu saukin rayuwa.
Sun ce yawaitar tashin man fetur din ya sanya Albashin su baya isa, wajen Siyen kayan abinci, kudin haya, kudin Makarantar yara da sauran bukatun yau da kullum.
Yanzu haka dai litar man Fetur ta kai kusan Naira 300 a birnin tarayyar Abuja, maimakon Naira 185 da ya kamata ace ana siyar da ita.
Sauran jihohin kasar nan na ci gaba da fama da dogayen layukan gidan mai, sakamakon yadda man yake karanci bayan ga tsada da yayi.
A wani labarin kuma: Yawancin hanyoyin Najeriya sun lalace – shugaban FERMA
Hukumar kula da tituna na tarayya ta ce galibin titunan Najeriya da manyan titunan kasar da ake ganin tarkon mutuwa ne a tsawon shekaru sun lalace kuma suna bukatar kulawa akai-akai.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar ta FERMA, Nuruddeen Rafindadi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Kaduna a wajen taron tunawa da Mahmud Armiya’u karo na 10 da bayar da kyaututtuka, wanda kungiyar Injiniya ta Najeriya reshen Kaduna ta shirya.
Laccar ta kasance takenta, ‘Batutuwan da suka shafi harkar sufuri.’
Comments 1