Ana ci gaba da samun rudani kan matsayar makarantu a Karamar Hukumar KAjuru na Jihar Kaduna bayan da gwamna Nasir el-Rufa’i ya yi umarnin cewa kada a rufe makarantu.
Toh sai dai Ma’aikatar ilmin jihar ta fitar da wata takarda dake umartar dukkannin makarantu a karamar hukumar da su rufe nan take biyo bayan ci gaba da samun barazanar tsaro a Karamar hukumar.
Umarnin yana zuwa ne yan kwanaki bayan da yan fashin daji suka yi garkuwa da dalibai da Malaman su a kauyen Rama dake Karamar hukumar Birnin Gwari.
Gwamna el-Rufa’i bayan wani taron da ya gudana a ranar Talata ya umarci dukkannin makarantu da kada su kuskura su rufe, inda ya sha alwashin maganin duk wasu bata gari masu burin kawo koma baya ga al’umma.
Karamar Hukumar Kajuru na daya daga cikin kananan hukumomi biyar dake fuskantar barazanar tsaro a Jihar.
“biyo bayan yawaitar samun matsalolin garkuwa da jama’a da kuma karin wasu matsalolin tsaro a wasu kauyuka na karamar hukumar Kajuru, Darakta Janar na Hukumar tabbatar da Ingancin Aiki ya umarce ni da na sanar da dukkannin makarantu kama daga na gwamnati har izuwa masu zaman kan su da su rufe daga ranar 16 ga watan Faburairun 2021” A Cewar takardar.
Ta Kara da Cewa “Kada wata makaranta ta kuskura ta bude har sai an sake bada umarnin ytin hakan”