By Ishaq Dabai
Majalisar Tattalin Arzikin Kasa tace Ma’aikatar Lafiya tana kafa tsirrai dan samun iskar mai kyau a cikin jihohi 36 na tarayyar kasar.
Gwamna David Umahi na Ebonyi shine wanda ya sanar da hakan ga manema labarai na Fadar Shugaban kasa bayan kammala wani taron NEC a ranar Juma’a.wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman tattaunawar da aka yi a Fadar Shugaban kasa.
Umahi yace Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, wanda ya jagoranci kwamitin NEC Adhoc da ke hulda da Kwamitin Shugaban Kasa (PTF) kan cutar COVID-19 don sauƙaƙe kullewar tattalin arziƙi, ya gabatar da rahoto ga majalisar.inda yace “Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya tana kafa tsirrai dan sanar da iskar shaka mai kyua wato (oxygen) a cikin jihohi 36 na kasar nan, amma a halin yanzu an samar da tsirran bishiyoyin ga jihohi shida dan samar da iskar mai inganci (oxygen) zuwa yanzu.
“Gwamnatin tarayya ta biya allurai miliyan 40 na alluran cutar COVID-19 dake shigowa rukuni-rukuni saboda haka adadi mai yawa na alluran zai shigo cikin kasar daga yanzu zuwa watan Janairu na sabuwar shekara 2022.”Yanzu Najeriya tana cikin jerin kasashe 50 na yankunan.”
Har yanzu Najeriya tana cikin rukunin farko na allurar rigakafin cutar kuma kayan aikin rigakafin za su inganta yayin da kasar ke samun karin alluran rigakafin.sannan Umahi yace an bukaci jihohi da su ci gaba da tura ayyukan gwaji don gano sabbin maganganu kafin lamarin ya tsananta.
Gwamnan yace majalisar ta kuma samu sabon bayani kan halin da ake ciki dangane da barkewar cutar kwalara.wadanda ake zargin sun kamu da cutar sun kai 88,704.acikin “Adadin jihohi 31 kuma harda babban birnin tarayya Abuja.Adadin wadanda suka mutu ya kai 3,208 a fadin kasar.
Kazalika ya bayyana cewa akwai ƙalubale sosai musamman ma wajen wahalar shiga wasu al’ummomin saboda rashin tsaro, da najasa da kuma rashin ruwan sha mai kyau.