An tabbatar da mutuwar wani Fasto da matarsa da wani mutum daya, a wani hadarin mota daya afku a kan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri, da ke jihar Bauchi.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa shiyar Bauchi FRSC, Yusuf Abdullahi ne wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a garin Bauchi, inda ya ce, hatsarin ya faru ne ranar Juma’ar data gabata, da misalin karfe 2:30 na dare, kimanin kilomita 12 daga ofishin hukumar FRSC dake Darazo.
Abdullahi ya ce, an kai wadanda abin ya rutsa da su babban asibitin garin Darazo, inda a nan ne aka tabbatar da mutuwarsu.
Ya alakanta musabbabin hatsarin da ketare Mota ba bisa ka’ida ba wato Overtaking, wanda ya rutsa da Mota kirar Citron Wagon mai lamba kamar haka: BAU 569 AA.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kamfanin Jiragen sama na Ethiopian Airways zai fara aiki a Enugu
Kazalika ya ce, faston da matarsa suna aiki ne da wani kamfani mai zaman kansa, Mai suna Gino Company, inda suke kan hanyar su ta zuwa Azare don tallata Kamfanin, lokacin da hatsarin ya rutsa da su.
A karshe Abdullahi ya ce, za a mika jimillar Naira 21,000 da aka samu a inda hadarin ya faru, ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.
A wani labarin Kuma na daban
Yan bindiga sun kashe mutane biyar, tare da jikkata wasu biyar, a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a kauyen Uchukku da sanyin safiyar Juma’a, kuma a yayin da suke satar shanu, Yan bindigan sun harbe mutane biyar har lahira.
Wani mazaunin garin Shanga, shelkwatar karamar hukumar Shanga, Yushau Garba Shanga, ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 1:50 na safe.
Ya kara da cewa hudu daga cikin wadanda aka kashe sun mutu nan take, yayin da daya daga cikin wadanda suka jikkata ya mutu ya mutu a asibiti.
A cewarsa, an kwantar da mutanen da suka jikkata a wani asibiti dake garin Shanga, domin kula da lafiyarsu.
Ya ce, daga cikin wadanda suka jikkata, har da wata karamar yarinya da aka harba a kafa.
Kazalika ya ce, mazauna yankin da abin ya shafa, sun bar yankin yayin da mafi yawansu suka koma Shanga donmin neman tsira.
“Mutum biyar da aka kashe yan gida daya ne. Dukansu ‘yan’uwan juna ne” inji shi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kebbi DSP Nafiu Abubakar, bai dauki kiran wayar da aka kai masa ba, kuma bai amsa sakon kartakkwana ba.