By Abbas Yakubu Yaura
An kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a maboyar su da ke kusa da unguwar Ossra-Irekpeni da ke kan titin Okene-Lokoja zuwa Abuja.
Daya daga cikin mafarautan yankin da suka kai harin ya shaida wa Jaridar Aminiya cewa an yi musayar wuta a tsakanin su da ‘yan bindigar.
Majiyar tace mafarautan tare da shugaban karamar hukumar Adavi ta Kogi, Joseph Samuel Omuya, sun kai farmaki cikin dajin ne bisa samun labaran sirri da suka yi, da yammacin Laraba.Majiyar ta ce yayin da suke kokarin shiga dajin, masu garkuwar sun bude wuta inda mafarautan suka mayar da martani tare bude wuta a kan ‘yan bindigar.
“Nan take sai muka yi ta harbe-harbe sannan aka kama uku daga cikin masu garkuwa da mutane,” inji shi.
A cewarsa, wasu ‘yan kungiyar sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da wadanda aka kama aka mika su ga jami’an tsaro a Lokoja, babban birnin jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaban karamar hukumar Adavi ya tabbatar da kama wasu masu garkuwa da mutane uku, inda ya ce shi ne ya jagoranci aikin. Sannan Ya ce masu garkuwa da mutanen na daga cikin ’yan kungiyar da ke addabar mazauna yankin da matafiya a kan babbar hanyar Okene-Lokoja zuwa Abuja.
“Daya daga cikin masu garkuwa da mutane ya bayyana yadda suke gudanar da ayyukansu, da irin nagartattun makaman da suke amfani da su, ya kuma lissafa sunayen wasu ‘yan kungiyar,” in ji shi.
Shugaban, ya ya yabawa mafarautan yankin bisa kokarinsu da kuma jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu, ya bukaci mazauna kauyukan da su kasance masu kula da harkokin tsaro tare da bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro da suka dace.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran waya ko amsa sakon da aka aike masa ba kan lamarin.