Dubban magoya bayan Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, a ranar Asabar a Ibadan, sun gudanar da zanga-zanga, suna kira da a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
A halin yanzu Igboho na tsare a Jamhuriyar Benin bisa wasu batutuwan da suka shafi hijira ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu.
Masu zanga-zangar wadanda galibinsu matasa ne, na dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban, inda suka bukaci a gaggauta sakin dan gwagwarmayar da ke hannun jamhuriyar Benin.
Sun fara zanga-zangar ne daga gidan Igboho da ke Unguwar Soka a Ibadan inda suka yi dafifi a kan Titin Toll Gate da ke kan titin Ibadan zuwa Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 2 Sun Mutu 15 sun Jikkata Yayin Hadarin Mota a Hanyar Legas Zuwa Ibadan
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa matasan da suka gudanar da zanga-zangar na rera wakokin hadin kai ne, inda suke kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen ganin an sako Igboho daga hannun jamhuriyar Benin.
Daya daga cikin masu zanga-zangar, mai suna Kareem Adesope, ya bukaci shugabannin Yarbawa da sauran ‘yan Najeriya, da su yi galaba a kan gwamnatin tarayya wajen ganin an sako dan gwagwarmayar.
Adesope ya ce labarin baya-bayan nan na cewa dan fafutukar ba shi da lafiya, ya kamata ya zama abin damuwa ga dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa, yana mai cewa, bai kamata a bar dan gwagwarmayar ya mutu a tsare ba.