Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Majalisar Tarayyar kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka, Dr Sidie Tunis, ya ba da umarnin dakatar da daukar ma’aikata cikin gaggawa.
Daga baya ya kafa kwamitin da zai binciki kurakuran da ake zargin antafka wajen daukar ma’aikata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Sun Kara Mai Zuwa APC A Jihar Kebbi
Tunis ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa da sashin sadarwa na majalisar ya fitar.
Dakatarwar ta biyo bayan zargin da tawagar Najeriyar ta yi a zauren majalisar cewa an mayar da ‘yan takarar kasar saniyar ware a aikin daukar ma’aikata.
Wakilan Najeriya a kungiyar sun yi barazanar janyewa daga zama mamba a majalisar yayin da ake mayar da ‘yan kasar saniyar ware a majalisar ta fuskar aiki da kuma karin girma.
Shugaban majalisar ya samu korafe-korafe a rubuce daga mataimakin shugaban majalisar na farko, Hon. Ahmed Idris Wase da wakilin dindindin na Najeriya a hukumar ECOWAS, Ambasada Musa Sani Nuhu.
A cewar sanarwar, ana sa ran kwamitin bincike mai zaman kansa na mutum takwas zai fara aiki a watan Agustan 2022 kuma ana sa ran bayyana sakamakon binciken ga shugaban majalisar a cikin mako guda.
Za a kira taron ofishin cikin gaggawa don yin la’akari da rahoton gabatar da taron gaba ɗaya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “ Matakin da mai girma kakakin ya dauka ya yi daidai da ka’idar doka ta talatin da uku (33) data talatin da hudu (34) na dokokin majalisar wanda ya tanadi kafa wani kwamiti na musamman da zai yi magana ta musamman akan al’amuran.
“Kwamitin na wucin gadi zai kasance karkashin jagorancin Sen. Mohammed Ali Ndume, shugaban kwamitin gudanarwa, kudi, da kasafin kudi.
“Sauran Mambobin Kwamitin sun hada da: Hon. Lynda Chuba Ikpeazu daga Najeriya da Hon. Fatoumatta Njai daga kasar Gambia.
“Hon. Amadou Djibo Ali daga Nijar, Hon. Kounon Nahou Agbandao daga Togo, Hon. Caramo Camara daga Guinea Bissau, Hon. Moussokora Chantal Fanny daga Cote d’Ivoire da Mista Arboncana Oumarou Dicko don zama magatakarda ga kwamitin.
“Sharuɗɗan kwamitin wucin gadi za su kasance kamar haka: Bincika zarge-zargen da ba su dace ba a cikin ayyukan da ake yi a Majalisar ECOWAS; Bincika zarge-zargen mayar da ‘yan takarar Najeriya saniyar ware a tsarin daukar ma’aikata na yanzu;
“Bincike tare da tantance ko da gaske majalisar ta amince da wani kuduri game da batun (daukar ma’aikata), ta hanyar amfani da tsarin majalisar;
“A yayin aiwatar da aikin sa, kwamitin za a ba shi damar samun duk wasu takardu da suka shafi aikin daukar ma’aikata da kuma yin aiki tare da kwamitin ba da shawara kan daukar ma’aikata da kara girma a majalisar ECOWAS, don yin karatu da duba aikin.
“Kwamitin na wucin gadi zai kasance ne ta hanyar tanade-tanaden Dokar Kari da ka’idojin Ma’aikatan ECOWAS.”
Shugaban majalisar ya ce ya dukufa wajen tabbatarwa da kare hakkin duk wani dan kasa na neman mukamai a kowace cibiya ta ECOWAS, daidai da tanade-tanaden dokokin ma’aikatan kungiyar da duk wasu ka’idoji masu alaka.
(NAN)