Wani mai daukar hoto Ismail Sanusi, a halin yanzu yana fafutukar kare rayuwarsa bayan wasu bata garin da dama sun kai masa hari tare da caka masa wuka a lokacin da yake nadar yadda halin da ake ciki ke faruwa a kan babbar hanyar Apapa-Oshodi da kuma kusa da tashar jiragen ruwa na Apapa da Tin Can a jihar Legas.
Baya ga shi, ma’aikatan gidan talabijin na Arise TV, wadanda suma suna cikin bakin kokarinsu don ganin an sassauta zirga-zirga a tashoshin jiragen ruwa, an ce sun bace bayan wasu bata gari sun kai musu hari don dakatar da faifan bidiyo a kan ma’aunin Apapa.
Har yanzu ba a san inda suke ba.
‘Yan iskan da suka kai wa ‘yan jarida hari a yau, sun hada da kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa, kungiyar masu daukan ma’aikatan sufurin jiragen ruwa ta Najeriya, da ma’aikatan ruwa, da kuma wadanda karamar hukumar Apapa ke yiwa masu ababen hawa a hanya.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ismail Sanusi dan jarida ne a gidan talabijin na Channels TV.