Nafisat Muideen, mahaifiyar jaririya mai watanni 5 da karen Alsatian ya kashe a unguwar Hallelujah Estate, Osogbo, Osun a ranar Laraba, ta ce ba a samu ceto kan lokaci ba yayin harin.
Misis Muideen, mai shekaru 28, ta bayyana irin halin da ta shiga yayin da take zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a gidanta ranar Alhamis a Osogbo.
Mahaifiyar da ke cikin bakin ciki ta bayyana cewa an kai mata hari ne da misalin karfe 1:45 na rana a kan hanyarta ta zuwa wani kantin sayar da magani domin siyo wa diyarta mara lafiya magani.
Ta ce a kan hanyarta ta zuwa shagon sayar da magunguna ne ta ji karar kare a baya, nan take ta juya baya, sai karen ya yi mata tsalle ya far wa jaririyar da ta makale a bayanta.
KARANTA NANDa Babu Kasar Faransa Da Tuni Mali,Burkina Faso Da Nijar Sun Zama Tarihi-Macron
A cewarta, kare ya ciro jaririn daga baya kuma a lokacin da take kokarin ceto jaririn, kare ya rinjaye ta saboda karen yana da girma.
Ta ce babu kowa a kusa da ita lokacin da aka kai mata hari kuma a lokacin da mutane suka fito don ceto ta, kare ya kashe jaririyar.
Na fita dauke da jaririna a baya don in samo wa kaina da jaririn kwayoyi,akan hanyata ta fita, sai na ji karar daga baya, lokacin da na juya don dubawa, sai wani kare ya yi tsalle daga baya ya afka wa jaririn.
Mutanen da suka zo cetona sun yi nasarar kashe karen, amma a lokacin da aka ciro jaririna daga karkashin kare, ta riga ta mutu ta bayyana tana kuka.
Mista Muideen ta ce bayan harin an kai ta wani asibiti da ke kusa kafin daga bisani a kai ta asibitin ‘yan sanda da ke Oke-Fia a Osogbo domin yi mata magani.
Haka kuma, mijin matar Oyegbade Muideen, ya bukaci a gano ainihin mai karen.
Adekola Timothy, mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A WANI LABARIN KUMAKu Dauki Sabbin Sojoji Aiki Wadanda Kenan Sun Gaji- Masana Ga Gwamnatin Tarayya
Eh, lamarin ya faru kuma a halin yanzu yan sanda suna neman mai karen in ji shi.
NAN ta samu labarin cewa karen wanda ya kashe ya tsere daga kejin sa, a wani gini da bai kammala ba kusa da gidan wanda aka kashe.