Uwargidan shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta Ziyarci zauren majalisar dattawa, a safiyar yau Laraba, domin shaida yadda zata wakana Kan zaman kwamitin nazarin kundin tsarin mulkin kasa, na 1999. Wanda kuma zai gabatar da rahoton, da ya tattara.
Aisha Buhari ta samu rakiyar ministocin kudi da harkokin mata, Zainab Ahmed da Pauline Tallen, Sai kuma jami’an Tsarota.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya tarbi uwargidan shugaban kasa da tawagarta zuwa Red Chamber da misalin karfe 11:58 na safe.