Mai Martaba Sarkin Kano Ya Bukaci Gwajin Kwaya Ga Masu Rike Da Makamai
Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su samar da sabbin dokoki na gwajin kwaya na tilas a kan duk wanda ke neman mukamin gwamnati a kasar nan.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron yini guda kan shaye-shayen miyagun kwayoyi da rashin tarbiyya da aka gudanar a sabon dakin taro da ke Jami’ar Arewa maso Yamma a Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN:Amurka Ta Ya Yi Kira Da A Gaggauta Sakin Bazoum
Sarkin ya jaddada bukatar gwamnati kan yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi, da suka hada da abubuwa kamar zakami, gadagi, da Tramol, da dai sauransu.
Ya nuna rashin jin dadinsa da yadda ake samun yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi da suka shafi masu rike da mukaman gwamnati a kasar.
“Ya kamata gwamnatoci a dukkan matakai su samar da sabbin dokoki kan shaye-shayen miyagun kwayoyi tare da sanya duk wanda ke neman mukamin gwamnati a yi masa gwajin miyagun kwayoyi na tilas.” Sarkin ya bayyana.
A halin da ake ciki, Sarkin ya yi kira ga Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya, FRSC da ta gaggauta tura karin jami’ai domin dakile tukin ganganci a cikin babban birnin Kano.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon kwamandan sashen na jihar Kano, Ibrahim Sallau Abdullahi, a fadarsa ranar Laraba.
Ya bukaci mazauna yankin da su bi doka da oda, ta yadda za a karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Yobe Ta Kaddamar Da Dashen Itatuwa Da Rigakafin Cutar Anthrax
Makwanni kalilan da suka wuce ne aka bayyana cewa wata cutar dabbobi da ake kira Anthrax ta barke a wasu sassan Afrika wanda Najeriya ma tana daga ciki.
Cutar tana iya yaduwa daga dabbobi kuma ta kama mutane ta hanyoyi daban-daban.